Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan wasan Najeriya na neman a biya su hakkinsu

‘Yan wasan kungiyar kwallon kafar Najeriya ta mata, Super Falcons sun jajirce kan neman hakkokinsu daga hukumar kwallon kafar kasar , in da suka bayyana cewa ba za su fice daga Otel din da aka ajiye su a birnin Abuja ba, har sai an biya su alawus na lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika ta mata da aka gudanar a Kamaru.

Tawagar super falcons da ta lashe kofin nahiyar Afrika na mata a Kamaru
Tawagar super falcons da ta lashe kofin nahiyar Afrika na mata a Kamaru
Talla

‘Yan wasan na bukatar hukumar NFF ta biya kowanne daga cikin su kimanin Dala dubu 17 da 150 saboda nasarar da suka samu ta lashe kofin a karo na takwas.

Rahotanni sun ce, a can baya, hukumar NFF ta yi alkawarin biyan ‘yan matan Dala dubu 6 da 500 na samun nasarar shiga gasar a Kamaru, amma aka gaza biyan su.

A halin yanzu dai ‘yan wasan na bukatar a biya jumullar Dala 23 da 650 ga kowanne mutun guda daga cikinsu.

Daya daga cikin ‘yan wasan ta bayyana cewa, ba za su fice daga Otel din Agura da ke Abuja ba domin kuwa yin haka, tamkar zubar da damarsu ce ta karbar hakkokinsu.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.