Isa ga babban shafi
Wasanni

An mika wa Chapecoense kofin Sudamericana

Hukumar kwallon kafar kudancin Amurka ta bai wa kungiyar Chapecoense kofin gasar Copa Sudamericana bayan akasarin 'yan wasan kungiyar sun gamu da ajalinsu a hatsarin jirgin sama da ya ritsa da su a Colombia.

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Chapecoense ta Brazil
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Chapecoense ta Brazil REUTERS/Paulo Whitaker
Talla

‘Yan wasan kungiyar 19 ne suka rasa rayukansu a hatsarin na makon jiya kuma a dai dai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wasan karshe a gasar, in da suka yi shirin kece raini da Atletico Nacional.

Kungiyar Atletico Nacional ce ta bukaci a mika kofin ga Chapacoense, lura da lamarin ban tausayi da ya cika da ‘yan wasan.

A bangare guda, kimanin mutane 13 ne cikin kwanaki biyu, suka nemi a dauke su don ci gaba da buga wa Chapecoense kwallon kafa da ke Brazil.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.