Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta lashe gasar Afrika ta mata

Babbar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika ta mata da aka gudanar a Jamhuriyar Kamaru.  

Tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya ta lashe kofin Afrika a karo na takwas
Tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya ta lashe kofin Afrika a karo na takwas premiumtimesng.com
Talla

Kungiyar ta Super Falcons ta samu nasarar ce bayan da ta doke takwararta ta Kamaru, Indomitable Lionesses da ci daya mai haushi a wasan karshe da suka fafata a filin wasa na Ahmadou Ahidjo da ke birnin Younde.

Desire Oparanozie ce ta jefa kwallon tilo da ta bai wa Najeriya nasara.

Tuni dai shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya jinjina wa Super Falcons bisa wannan nasarar da ta samu a yau Aasabar.

Shugaba Buahri ya bayyana nasarar a matsayin abin farin ciki, yayin da a karo na takwas kenan da Najeriyar ke lashe wannan kofin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.