Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta jaddada bukatar samun nasara kan Najeriya

Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Kamaru, ta bukaci tawagar ‘yan wasan kasar da su tabbata sun samu nasara a wasan da zasu yi da Najeriya a cikin shekara mai kamawa.

'Yan wasan kwallon kafa na kasar Kamaru
'Yan wasan kwallon kafa na kasar Kamaru
Talla

Kiran na hukumar kwallon kafar Kamaru FECAFOOT na zuwa bayan da tawagar kasar, ta gaza samun nasara kan Zambia a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin Duniya da za’ayi a Rasha na 2018, inda aka suka tashi 1-1.

Najeriya ke jagorantar rukunin B da maki 6 bayan lallasa 6 Algeria da 3-1, sai Kamaru da ke biye mata da maki 2, yayinda Zambia da Algeria ke da maki 1 kowannesu.

Sai a ranar 28 ga watan Agusta da kuma 2 ga Satumba a shekara mai kamawa za’a fafata tsakanin Najeriya da Kamaru, abinda yasa hukumar kula da kwallon kafar kasar ke ganin suna da lokacin kimtsawa domin samun nasarar kan Najeriya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.