Isa ga babban shafi
EFL

Southampton ta fitar da Arsenal a gasar kofin EFL

Manchester United ta kai zagayen kusa da karshe a gasar lig cup ta Ingila bayan ta doke West Ham United ci 4-1 Yayin da kuma aka yi waje da Arsenal a gasar bayan ta sha kashi a hannun Southampton ci 2-0 a filin wasanta na Emirate.

Kocin Arsenal Arsene Wenger
Kocin Arsenal Arsene Wenger Reuters/Stefan Wermuth
Talla

Zlatan Ibrahimovic Anthony Martial ne suka jefa wa Manchester kwallayenta a ragar West Ham.

A wasan ne Bastian Schweinsteiger ya yi haskawar farko a kungiyar a bana inda aka sako shi ana dab da tashi wasan a Old Trafford.

Yanzu Manchester United za ta hadu ne da Hull City a zagayen kusa da karshe yayin da Southampton za ta kara da Liverpool a fafatawar da za su yi sau biyu a 10 da kuma 24 ga Janairun sabuwar shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.