Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Schweinsteiger ya dawo atisaye

Manchester United ta dawo da Bastian Schweinsteiger atisaye a babbar tawagar kungiyar bayan Mourinho ya mayar da kaftin din na Jamus saniyar-ware tun zuwan shi Old Trafford.

Bastian Schweinsteiger ya yi horo da 'Yan wasan Manchester United
Bastian Schweinsteiger ya yi horo da 'Yan wasan Manchester United manutd.com
Talla

Manchester United ta wallafa hoton Schweinsteiger a intanet yana atisaye tare da  sauran ‘Yan wasanta a yau Litinin.

Dan wasan dai ya koma dan kallo daga nesa bayan zuwan Mourinho a Manchester United inda ko a wasannin share fagen kaka da kungiyar ta buga da kuma wasannin Europa Lig ba a sa Schweinsteiger ba.

Kiran Schweinsteiger na zuwa ne bayan Manchester United ta buga wasannin Firimiya uku ba tare da nasara ba inda a karshen mako Burnley ta rike Mourinho babu ci 0-0 a Old Trafford.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.