Isa ga babban shafi
Wasanni

Har yanzu Rooney ne jagoran Manchester United- Smalling

Dan wasan baya na Manchester United, Chris Smalling ya bayyana cewa, har yanzu kaften din kungiyar, Wayne Rooney shi ne jagora a Old Trafford duk da ajiye shi da aka yi a banci a fafatawar da suka doke Leicester City da ci 4-1 a gasar Premier ta Ingila.

Dan wasan Manchester United, Wayne Rooney
Dan wasan Manchester United, Wayne Rooney Action Images/Reuters/Carl Recine
Talla

Smalling wanda ya ci kwallo guda a wasan ya ce, ko kadan Rooney bai ji haushin rashin saka shi a farkon wasan ba, har sai da aka kusan tashi da kimanin minti 10.

A karon farko kenan da kocin kungiyar Jose Mourinho ya ajiye Rooney a banci tun bayan da ya karbi aikin horar da kungiyar a wannan kakar, abin da ake ganin yana da nasaba da kashin da Manchester United ta sha sau uku a jere.

A halin yanzu dai, Rooney mai shekaru 30 na bukatar zura kwallaye hudu kacal don yin kan-kan-kan da Sir Bobby Charlton a matsayin wanda ya fi zura kwallaye a tarihin Manchester United.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.