Rome ya fasa daukar nauyin Olympics na 2024
Birnin Rome na Italiya ya bayyana kudirinsa na janyewa daga karban bakwancin wasannin Olympics a shekarar 2024.
Wallafawa ranar:
Magajiyar garin na Rome, Virginia Raggi wadda aka zaba a cikin watan Yulin da ya wuce, ta shaida wa maneman labarai cewa, ba za ta bari birnin ya kara tsindima cikin matsalar bashi ba.
A baya can, birnin ya janye daga daukan bakwancin gasar Olympics a shekarar 2020 saboda matsalar kudade, in da aka bai wa Tokyo na Japan.
Yanzu haka dai akwai biranen Paris da Los Angeles da Budapest da ke neman a basu izinin gudanar da wasannin na Olympics a shekara 2024.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu