Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Faduwar Jiragen sama dauke da ‘Yan wasa

Kasar Brazil ta fara zaman makoki kan hatsarin jirgin da ya hallaka mutane sama da 70 yawancinsu tawagar kungiyar kwallon kafar Chapecoense Real. Wannan dai ba shi ne hatsarin jirgin sama na farko ba da ke hallaka 'yan wasa.

Yan wasan Chapecoense a cikin jirgin sama kafin su yi hatsari
Yan wasan Chapecoense a cikin jirgin sama kafin su yi hatsari Photo: Facebook de
Talla

A shekarar 1949 wani jirgi mai dauke da tawagar kungiyar kwallon kafar Torino Grande ta Italiya ya fadi lokacin da ya bar Portugal inda ya kashe mutane 31.

A shekarar 1958, jirgin da ke dauke da ‘Yan wasan kungiyar Manchester United ya fadi bayan ya sha mai a birnin Munich, inda ya kashe mutane 23.

A shekarar 1961, kungiyar ‘yan wasan Amurka sun yi hatsari a wani jirgi da ya fadi a Belguim, bayan wani wasan da suka yi da kasar Czechoslovakia inda ‘yan wasa 18 suka mutu.

A shekarar 1972, kungiyar ‘yan wasan zari ruga ta Uruguay 40 sun mutu lokacin da jirginsu ya fadi akan hanyar zuwa Chile. Mutane 27 suka mutu nan take, sannan 11 suka mutu daga baya.

A shekarar 1987 wani jirgin Peru mai dauke da mutane 43 cikinsuu har da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar Alianza Lima, sun fada teku a Lima inda suka mutu.

A shekarar 1994 daukacin ‘yan wasan kwallon kasar Zambia sun mutu a wani hatsarin jirgin sama, sai Kalusha Bwalya kadai ya tsira shi da ba ya cikin jirgin.

A shekarar 2011 daukacin ‘yan wasan kungiyar kwallon gora na kankara na kasar Rasha 44 suka mutu akan hanyarsu ta zuwa Minsk.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.