Isa ga babban shafi
Duniya

Jirgin fasinja yayi saukar gaggawa a Dubai

Wani jirgin saman Emirates mai dauke da fasinjoji 300 yayi saukar gaggawa a filin sauka da tashin jiragen sama dake Dubai.

Jirgin fasinja yayi saukar gaggawa a Dubai
Jirgin fasinja yayi saukar gaggawa a Dubai Reuters
Talla

Rahotanni sun ce jirgin yayi saukar gaggawar ba tare da tayoyinsa sun fito ba, kuma an ga jirgin yana fitar da bakin hayaki kafin kaiwa ga kasa.

Dukkanin fasinjoji 300 dake cikin jirgin sun tsira da rayukansu, sai dai wani jami’in kashe gobara ya rasa ransa yayin kokarin aikin ceto.

Shugaban kamfanin na Emirates ya bayyana jimami kan mutuwar jami’in kashe gobarar.

Jirgin saman kirar Boeing 777 yana kan hanyarsa daga Dubai zuwa jihar Kerala dake kudancin kasar India yayin da ya sauya akalarsa.

Yanzu haka zirga zirgar jiragen sama ta cigaba da gudana a filin jiragen na Dubai bayan dakatar da hakan da aka yi na dan takaitaccen lokaci a baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.