Isa ga babban shafi

Za a biya dangin fasinjan EgyptAir diyya

Kamfanin Sufurin jiragen sama na Masar da ake kira EgyptAir zai biya iyalan fasinjoji 66 da suka mutu a hatsarin jirgin kamfanin a tekun Bahrum wanda ya taso daga Paris zuwa birnin Alkahira.

An tsinto tarkacen Jirgin EgyptAir a tekun Bahrum
An tsinto tarkacen Jirgin EgyptAir a tekun Bahrum HO / Egyptian military spokesperson's facebook page / AFP
Talla

EgyptAir zai biya wani kaso na kudaden diyyar da ya kai Dala 25,000 kowanne daga Fasinjan da suka mutu a cikin jirgin da ya yi hatsari.

Kudin ba shi da nasaba da kudaden inshoran da ake so kamfanin ya biya iyallan fasinjojin da suka rasa rayukansu, har sai an kammala binciken dalilin faduwar jirgin.

Jirgin kamfanin kirar Airbus da ya bar Paris zuwa Birnin Alkahira ya fadi ne ranar 19 ga watan Mayu.

Fasinjan jirgin sun hada da Misrawa 30 da Faransawa 15 da ‘Yan kasashen Iraqi dsa Canada da Belgium da Algeria da Portugal da Chadi da Saudiya da Sudan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.