Isa ga babban shafi
Masar

An ga tarkacen Jirgin EgyptAir a tekun Mediterranean

Masu Gudanar da bincike a kasar Masar sun ce sun gano tarkacen jirgin EgyptAir da ya yi hatsari a watan jiya a tekun Mediterranean dauke da mutane 66 a ranar 19 ga watan Mayu bayan tashin sa daga Paris zuwa birnin Alkahira.

Masu binciken Faransa sun gano wani tarkacen jirgin Masar da ya tarwatse a tekun Bahrum
Masu binciken Faransa sun gano wani tarkacen jirgin Masar da ya tarwatse a tekun Bahrum Egyptian Military
Talla

Kwamitin binciken jirgin a Masar ya fadi a cikin wata sanarwa cewa jirgin ruwan Faransa da ke aikin binciken jirgin ne suka gano tarkacen a wurare da dama a teku.

Masu bincike dai sun ce nan gaba kadan za su tantance dalilin da ya haifar da hatsarin jirgin.

Yawancin Fasinjan da ke cikin jirgin dai ‘Yan Egypt ne 30 da Faransa 15, sai kuma wasu ‘Yan Iraqi guda biyu da Canada biyu da kuma yan kasashen Algeria da Birtaniya da Portugal da Saudiya da Chadi da Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.