Isa ga babban shafi
Egypt- France

Sojan Ruwa na Faransa sun hango Naurar Nadan Magana na Jirgin Saman EgyptAir a teku

Sojan Ruwa na kasar Faransa dake cikin laluben akwatin nadan bayanai na jirgin Saman EgyptAir a tekun Bahrum, sun ce sun ji motsin akwatin nadan Magana na cikin Jirgin da zai taimaka sanin musabbabin faduwar jirgin.

Taswirar hanyar da jirgin saman EgyptAir ya bi
Taswirar hanyar da jirgin saman EgyptAir ya bi
Talla

Masu binciken musabbabin faduwar jirgin saman na EgyptAir na ganin tunda anji motsin akwatin nadan maganan, yanzu zaa kai mako daya kafin wani mutun-mutumi da za'a tura karkashin teku ya iya dauko naurorin  biyu da ake nema ruwa ajallo.

Shi jirgin saman na EgyptAir ya fada tekun ne bayan ya taso daga Paris na kasar Faransa zashi Alkahira na kasar Masara ranar 19 ga watan jiya, inda mutane 66 dake cikin jirgin babu wanda ya rayu.

Sojan ruwa na Faransa dake dawainiyar ciro naurorin, sun fadi cikin wata sanarwa cewa naurorin da ake zance na chan mita dubu 3 karkashin teku.

Wasu tarkacen jirgin saman dai an sami tsamo su tuni, ciki har da wasu kayayyakin fasinjojin jirgin.

Wasu bayanan na cewa akwai wani jirgin laluben karkashin teku na wani kamfani mai zaman kansa da akayi haya zai taimaka domin ganin a dauko akwatunan nadan bayanan jirgin ba tare da jinkiri ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.