Isa ga babban shafi
Brazil

Iran na jimamin dan tseren nakassasun kasar

Dan tseren keken na nakassasu ya rasa ransa ne bayan raunin da ya samu sakamakon munmunar faduwa da yayi a yayin da ake tsakiya gasar tseren keke a jiya asabar  a birnin Rio na kasar Brazil.

Bahman Golbarnezhad dan tseren keke na nakassasu ya rasu yana da shekaru 48
Bahman Golbarnezhad dan tseren keke na nakassasu ya rasu yana da shekaru 48 www.paralympic.org
Talla

Masu kai dokin gaggawa da likitoci sun yi iya kokarin ceto rayuwar gwanin tseren keken nakassasun mai suna Bahman Golbarnezhad ba tare da samun nasara ba.

Bahman dai dan asalin kasar Iran ne ya kuma mutu ne yana da shekaru 48 a duniya.

Sanarwar da kwamitin wasannin Olympics ta fitar, ta nuna alhininta kan mutuwar dan wasan, inda ta meka sakon ta’azziya ga kasar Iran da kuma iyalansa.

A yau ake kammala wasannin Paralympics ta na nakassasu bayan kwashe tsawon makonni biyu ana fafatawa a tsakanin ‘yan wasa daga kasashen duniya daban daban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.