Isa ga babban shafi
Wasanni

Kasuwanin tikitin wasanni Paralympics na Rio a Brazil

Rahotanni daga birnin Rio na Brazil sun ce an samu gagarumar nasara wajen yawan tikitin shiga kallon wasannin Paralympics, wato wasannin nakasasu ko kuma masu bukata ta musamman da ke gudana.

Wutar wasanni Paralympics na Rio  a Brazil
Wutar wasanni Paralympics na Rio a Brazil REUTERS/Pilar Olivares
Talla

A kalla sama da mutane dubu dari da saba’in ne suka yi tururuwar shiga kallon wasanni a satin da nuke bankwana da shi cikin rana guda hakan ya zarta yawan mutane 157,000 da aka gani a ranar da aka fara gasar.

Yanzu haka masana wasanni sun amince cewa gasar Paralympics ta wannan shekara ita ce a matsayi na biyu a cikin ire-irenta da aka taba yi a tarihi domin kuwa an saida tikitin kallon wasan sama da miliyan daya da dubu dari bakwai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.