Isa ga babban shafi
Wasan ninkaya

Mai yiwu Michael Phelps ya kara a wasannin Olympics na Rio

Shahararren dan wasan ninkayan nan kasar Amurka Michael Phelps ya ziyarci ofishin hukumar dake yaki da yin amfani da miyagun kwayoyi ta kasar Amurka, wanda hakan wasu ke cewa alama ce ta dake nuna cewa dan wasan zai koma fagen wasannin nikanya bayan ritaya da ya yi.

Michael Phelps lokacin da yake karawa a wasannin Olympics na London a bara
Michael Phelps lokacin da yake karawa a wasannin Olympics na London a bara Reuters/David Gray
Talla

A karshen gasar Olympic da aka gudanar na London ne dai Phelps ya bayyana ritayarsa bayan ya lashe kyautukan zinare guda hudu da kuma azurfa biyu.

Masu sharhi a fagen wasannin na kallon wannan lamarin a matsayin cewa Phelps yana shirin karawa ne a wasannin Olympics da za a birnin Rio de Janerio a shekara 2016.

Sai dai mai horar da dan wasan Bob Bowman ya ce kada mutane su cusa tsammanin zai dawo ne duk da cewa ya yi ritaya.

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.