Isa ga babban shafi
Wasanni

Al Ahly ta Masar na cikin tsaka mai wuya

Kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly da ke Masar ta shiga tsaka mai wuya a rukuninta na A a gasar cin kofin zakarun Afrika bayan da ta sha kashi ci 2-1 a gida a hannun ASEC Mimosas a fafatawar da suka yi a filin wasa na Borg El Arab a jiya Talata.

'Yan wasan Al Ahly ta Masar
'Yan wasan Al Ahly ta Masar AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

A karo na biyu kenan da kungiyar ke shan kashi a rukunin bayan da Zesco United ta casa ta a waje a wasansu na farko da suka yi a farkon wannan watan.

Wannan dai ya haifar da koma baya ga kungiyar wadda ke neman daukan kofin gasar a karo na takwas.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.