Isa ga babban shafi
Wasanni

Southgate zai horar da tawagar Ingila

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta shirya domin daukan Gareth Southgate a matsayin kocin rikon kwarya na tawagaar kasar bayan Roy Hodgson ya yi murabus saboda kashin da kasar ta sha a hannun Iceland da ci 2-1 a gasar cin kofn kasashen Turai da ake yi a Faransa. 

Gareth Southgate shi ne mai horar da tawagar kwallon Ingila ta matasa kasa da shekaru 21
Gareth Southgate shi ne mai horar da tawagar kwallon Ingila ta matasa kasa da shekaru 21 DR
Talla

Yanzu haka Southgate zai jagoranci ‘yan wasan na Ingila a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara ta 2018 a kasar Rasha.

Hukumar kwallon kafar dai, za ta ci gaba da neman wanda za ta bai wa aikin din-din-din na horar da ‘yan wasan kuma ana ganin hakan zai dauki tsawon watanni kamar yadda Martin Glenn, shugaban hukumar ya shaida wa manema labarai.

Mr. Glenn ya kara da cewa, da yiwuwar ma mace za su dauka domin ci gaba da horar da zaratan ‘yan wasan Ingila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.