Ronaldo ya ceto Portugal
Cristiano Ronaldo ya taimakawa Portugal tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin Turai bayan sun sha da kyar 3 da 3 a karawarsu da Hungary. Iceland ta tsallake bayan ta doke Austia 2 da 1.
Wallafawa ranar:
Kwallaye biyu Cristiano Ronaldo ya jefa a raga wanda yanzu shi ne dan wasa na farko da ya ci kwallaye a gasar cin kofin Turai karo hudu.
Haka ma Ireland ta samu wuri a zagaye na biyu bayan ta doke Italia 1 da 0
Belgium ta doke Sweden ci 1 da 0, wasa na karshe da Zlatan Ibrahimovic ya bugawa Sweden bayan tabbatar da zai yi ritaya idan an kammala gasar euro.
Sai a ranar Asabar za a soma fafatawar zagaye na biyu inda Switzerland za ta kara da Poland. Wales kuma da Nothern Ireland, Croatia da Portugal.
A ranar Lahadi ne kuma Faransa za ta kara da Jamhuriyyar Ireland a Lyon, Jamus da Slovakia a Lille
A Toulouse ne kuma Hungary zata kara da Belgium
Sai a ranar Litinin a kece raini tsakanin Italiya da Spain a Stade de France a Paris.
A Nice ne a ranar Litinin Ingila zata kara da Iceland.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu