Isa ga babban shafi
Copa America

Chile za ta hadu da Argentina a Copa America

Kasar Chile ta kai zagayen karshe a gasar Copa America bayan ta doke Colombia 2-0 a fafatawar da suka yi daren jiya Laraba. Yanzu kuma Chile za ta hadu ne da Argentina a wasan karshe, a ranar Lahadi.

A cikin ruwa aka yi wasan Chile da Colombia a gasar Copa America.
A cikin ruwa aka yi wasan Chile da Colombia a gasar Copa America. REUTERS
Talla

Chile da Argentina za su sake haduwa ne kamar yadda suka hadu a bara inda Chile ta lashe kofin.

An dai shafe kusan sa’o’I hudu kafin kammala wasan Chile da Colombia a jiya saboda tsawa da ruwan sama da aka yi samu a Chicago.

Ruwan saman ya sa ‘Yan kallo sun watse domin samun mafaka a rumfar filin wasan.

An dakatar da wasan na Kusan sa’o’I biyu da rabi kafin ‘yan wasan suka koma fili suka idar da wasan a cikin ruwa.

Sai dai an yi bige bige a wasan inda alkalin wasa ya ba da katin gargadi 8 da jan kati guda ga dan wasan Colombia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.