Isa ga babban shafi
Copa America

Brazil ta lallasa Haiti 7 da 1

Brazil ta lallasa Haiti ci 7-1 a gasar copa America ta Centenario da suka buga a daren jiya Laraba. Wannan ne karon farko da Haiti ta samu shiga gasar, kuma sakamakon wasanta da Brazil ya nuna an fitar da ita a gasar da ake bikin cika shekaru 100 da somawa.

Kwallaye uku Philippe Coutinho na Liverpool ya jefa a ragar Haiti a gasar Copa America
Kwallaye uku Philippe Coutinho na Liverpool ya jefa a ragar Haiti a gasar Copa America REUTERS
Talla

Kwallaye uku Coutinho na Liverpool ya jefa a ragar Haiti.

A daya bangaren kuma Peru da Ecuador sun tashi ne ci 2 da 2.

Yanzu kuma Brazil ce saman teburin rukuninsu na B da tazarar kwallaye tsakaninta da Peru da suke da maki 4.

A yau ne kuma Venezuela zata fafata da Uruguay a rukuninsu na C. Mexico kuma za ta fafata ne da Jamaica.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.