Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA na neman diyya daga jami'anta

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bukaci tsoffin jami’anta da ke fuskantar tuhuma a Amurka su biya ta miliyoyin daloli a matsayin diyya ga bacin sunan da suka janyo wa hukumar.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino. REUTERS/Hannah McKay
Talla

Akan haka FIFA ta bukaci a kwato ma ta kudaden daga tsoffin shugabanninta a matsayin diyya ga bacin sunan da suka janyo wa hukumar.

A cikin sanarwar da ta fitar FIFA ta ce, miliyoian daloli ne aka karkatar ta hanyar cin hanci da rashawa tsakanin jami’an hukumar.

Tsoffin jami’an FIFA 39 Amurka ke tuhuma da karbar cin hancin makudan kudade da ya kai dala biliyan 200.

Cikin wadanda ake tuhuma sun hada da toshon mataimakin shugaban FIFA Jeffrey Webb

FIFA na son Amurka ta mika ma ta cikin dala miliyan 190 da aka karba daga hannun tosffin jami’anta da wasu kamfanoni guda biyu.

FIFA ta zayyana sunayen wasu manyan tsoffin jami’anta a kwamitin zartarwar hukumar cewa, sun karbi kudi dala miliyan 28.

FIFA ta ce, tana son a dawo mata da kudaden, kamar yadda shugaban hukumar Gianni Infantino ya fada wanda aka zaba makwanni biyu da suka gabata.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.