Isa ga babban shafi
Premier

Wenger ya lallashi ‘Yan Arsenal

Arsene Wenger ya lallashi magoya bayan Arsenal su jingine boren da suka kudurta yi a babbar kawarar da kungiyar za ta yi da Leicester City a ranar Lahadi saboda tsadar farashin shiga kallon wasannin a gasar Firimiya.

Arsene Wenger na Arsenal
Arsene Wenger na Arsenal Reuters/Paul Childs
Talla

Hakan ta faru da Liverpool inda magoya bayanta suka fice a filin wasan a lokacin da ta ke fafatawa da West Ham saboda adawa da tsadar farashin kudin shiga kallon wasa.

Magoya bayan Arsneal ma sun sha alwashin yi wa kungiyarsu bore a ranar Lahadi, domin sai mutum ya biya kusan fam 100 domin yankar tikitin shiga kallon wasan kungiyar.

Magoya bayan Leicester ma sun ce zasu jinkirta shiga filin wasan Emirate na minti biyar da soma wasan.

Amma kocin Arsenal Arsene Wenger ya bukaci magoya bayan kungiyoyin biyu su janye shrin bore musamman kin shiga fili kafin soma wasan da kuma ficewa kafin kammalawa.

Wasan dai zai ja hankali saboda Leicester ce ke jagorancin Firimiya Lig, da tazarar maki 5 tsakaninta da Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.