Isa ga babban shafi
Premier

Chelsea ta doke Arsenal

Arsene Wenger ya mayar da martani kan zancen da wasu ke yi akwai Katanga tsakaninsu da Chelsea bayan a jiya Lahadi Arsenal ta sake shan kashi ci 1 da 0 a Emirates.

Diego Costa ne ya ci Arsenal
Diego Costa ne ya ci Arsenal Reuters / Dylan Martinez
Talla

Kusan wasanni tara a Firimiya Lig Arsenal ba ta samu galaba akan Chelsea ba, akan haka kuma wasu ke ganin Chelsea ta yi wa arsenal katangar karfe.

Sai dai kuma kocin kungiyar Arsene Wenger yace wasan jiya ya banbanta domin ana minti 18 da fara wasa aka ba dan wasan shi Mertesacker can kati bayan ya bige Costa.

Sannan Wenger ya yaba wa ‘yan wasan shi domin an kare wasan ci 1 da 0 sabanin ci 3 ko 4.

Yanzu dai Arsenal ta barar da damar darewa teburin Firimiya inda yanzu ta dawo a matsayi na uku. Leicester city ce yanzu saman tebur da tazarar maki uku tsakaninta da City da ke matsayi na biyu da kuma Arsenal a matsayi na uku.

A ranar Asabar, Southampton ta samu galaba akan Manchester United ci 1 da 0 a old Trafford, West ham kuma ta rike Manchester City ne ci 2 da 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.