Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi da Neymar ba za su buga wa kasashensu wasanni ba.

A gobe Alhamis ne kasashen yankin kudancin Amurka za su fara wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da Rasha za ta dau bakwanci a shekara ta 2018 yayin da kasashen Argentina da Brazil za su fara wasanninsu ba tare da zaratan yan wasansu ba wato Messi da Neymar. 

Neymar da Messi
Neymar da Messi Reuters
Talla

Messi dan asalin Kasar Argentina na fama da rauni yayin da Neyma na Brazil aka haramta masa buga wasnni hudu bayan an bashi jan kati a wasan da Brazil ta kara da Columbia a gasar Copa America da ta gabata.

kawo yanzu dai ya rasa wasanni biyu kuma saura wasanni biyu nan gaba da ba zai samu damar buga wa ba.

Ita ma kasar Uraguy za ta fara wasanta ba tare da Luiz Suarez ba da Edison Cavani kamar yadda ita ma Columbia za ta fafata ba tare da James Rodriguez ba wanda ke fama da rauni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.