Isa ga babban shafi
Wasanni

Jadawalin wasan dab da karshe na zakarun Afrika

An fitar da jadawalin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika.

Tambarin gasar cin kofin zakarun Afrika.
Tambarin gasar cin kofin zakarun Afrika.
Talla

A gobe asabar, kungiyar Zamalek ta kasar Masar za ta fafata da Etoile Sahel ta Tunisia.

A wasan su na zagayen farko dai, Etoile Sahel ce ta lallasa zamalek da ci 5-1.

A  ranar Lahadi kuma Alhaly ta Masar, wadda ke rike da kambi, za ta kara da Orlando Pirtaes ta Afrika ta kudu.

A wasansu na zagayen fako Orlando Pirate ce ta yi nasara da ci daya mai ban haushi.

Kawo yanzu dai dan wasan Etoile Sahel, Bounedjah shine ya fi zura kwallaye a gasar ta cin kofin zakarun Afrika, inda yake da kwallaye 7 sai kuma Ambourouet na kungiyar Mounana ta Gabaon dake bin shi da kwallaye 6.

Yayin da shima Mubele na Vita Club ta Jamhuriyar Demokradiyar Congo, da Salami na Worri wolves ta Najeriya ko wannen su ke da kwallaye biyar biyar.

Sai kuma masu kwallaye hur hurdu da suka hada Erasmus da Gabuza da Manyisa dukkanin su daga Orlando Pirates.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.