Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta sha kashi a wasanta na farko

Arsenal ta sha kashi a wasanta na farko da aka buga a gidanta, inda West Ham ta lallasa ta ci 2 da nema a ranar lahadi.

Arsene Wenger a hannun dama, yana nadamar shan kashi a wani wasa da suka buga.
Arsene Wenger a hannun dama, yana nadamar shan kashi a wani wasa da suka buga. REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Manajan Arsenal Arsene Wenger, ya ce ya damu matuka a game da wannan kashi da suka sha a jiya, duk da cewa daga farko har zuwa karshe, ‘yan wasansa ne suka mamaye filin kwallo da kuma samun dama fiye da abokannin karawarsu na West Ham.
Shi kuwa manajan West Ham Slaven Bilic ya kasance a cikin farin ciki ne sakamakon wannan nasara, domin kuwa ita ce ta farko da ya sama daga lokacin da ya karbi aikin horas da ‘yan wasan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.