Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

PSG ta diba lafiyar Di Maria

Paris Saint Germain ta diba lafiya Angel Di Maria na Manchester United a birnin Doha, inda dan wasan ke daf da barin Old Trafford duka shekara guda da United ta saye shi akan kudi kusan fam miliyan 60.

Angel Di Maria sanye da rigar Argentina
Angel Di Maria sanye da rigar Argentina
Talla

Dan wasan ya tafi Qatar ne domin tattaunawa da jami’an PSG, sannan kuma a diba lafiyarsa.

Kuma rahotanni sun ce Manchester United da PSG sun amince da fartashin dan wasan akan kudi kusam Fam miliyan 44 da rabi, kimanin yuro miliyan 63.

A bara ne dai Manchester ta karbo Di Maria daga Real Madrid, amma dan wasan ya yi fama da rauni, inda tauraronsa ya dushe.

zuwansa kwallaye hudu ya jefa a raga tare da taimakawa a zira kwallaye 6

Dan wasan ya shaidawa wata kafar wasanni cewa ya ji dadin komawarsa Faransa, tare alkawalin zai taimawa PSG tsallake wa zuwa zagayen daf da na karshe a gasar zakarun Turai, matakin da ya gagari kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.