Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Di Maria ya yi wa PSG tsada

Kungiyar PSG tace Di Maria ya yi tsada don haka ta fice daga tattaunawa da Real Madrid akan makomar dan wasan na Argentina. Shugaban kungiyar PSG Nasser al-Khelaifi yace ya tattauna da shugaban Real Madrid Florentino Perez, kuma ya fada masa cewa Di Maria ya wa PSG tsada akan kudi da suka kai euro Miliyan 60.

Angel de Maria, na Real Madrid
Angel de Maria, na Real Madrid REUTERS/Ivan Alvarado
Talla

PSG dai tana taka tsantsan ne don gudun keta dokokin kwallon Turai na fatali da kudaden domin sayen ‘Yan wasa bayan ta fuskanci hukunci da ita da Manchester City da attajiran Qatar ke shugabanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.