Isa ga babban shafi
Copa America

Argentina ta lallasa Paraguay

Argentina ta kai zagayen karshe a gasar Copa America bayan ta lallasa Paraguay 6 da 1 a daren jiya Talata. Duk da Messi bai jefa kwallo a raga ba, amma ya taka rawa a kwallayen da Angel Di Maria da Marcos Rojo da Javier Pastore da Sergio Aguero da Gonzalo Higuain suka jefa a ragar Paraguay.

Messi na Argentina yana karabkiya da Paulo da Silva na Paraguay
Messi na Argentina yana karabkiya da Paulo da Silva na Paraguay REUTERS/Mariana Bazo
Talla

Yanzu Argentina za ta hadu ne da Chile a wasan karshe a ranar Assabar .

Argentina dai na harin lashe kofin gasar ne na kasashen kudancin Amurka a karon farko tsawon shekaru 22.

Messi ya bayyana farin cikinsa akan yadda suka taka leda a jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.