Chile ta doke Ecuador a Copa America
Kasar Chile ta doke Ecuador ci 2 da 0 a gasar Copa Ameria ta kasashen yankin kudancin Amurka da aka fara a gudanarwa a Chile jiya Alhamis. Arturo Vidal da Eduardo Vargas ne suka jefa wa Chile kwallayenta a ragar Ecuador.
Wallafawa ranar:
Wannan ne karo na 44 da ake gudanar da gasar a Chile kuma Kasashe 12 ne ke haskawa a gasar.
Gasar ta kunshi manyan kasashe da suka hada da Argentina da Brazil da kuma Uruguay da Mexico.
Ido dai zai koma ne ga ‘Yan wasan Barcelona guda uku Messi wanda zai jagoranci Argentina da Neymar na Brazil da kuma Luis Suarez na Uruguay
Messi na harin lashe kofin ne karo na farko.
Baya ga Messi da Neymar da Suarez, gasar na kunshe da zaratan ‘Yan kwallo da ke sharafi a Turai, Irinsu James Rodriguez na Colombia da Alexis Sanchez na Chile Edinson Cavani na Uruguay.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu