Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Barcelona ta kai zagayen karshe a gasar Zakarun Turai

Barcelona ta tsallake zuwa zagayen karshe a gasar zakarun Turai bayan ta yi waje da Bayern Munich da jimillar kwallaye 5 da 3. Amma a fafatawar da suka yi jiya Talata Bayern Munich ce ta doke Barcelona 3 da 2, bayan Barcelona ta lallasa ta 3 da 0 a karawa ta farko.

Barcelona ta tsallake zuwa zagayen karshe a gasar Zakarun Turai
Barcelona ta tsallake zuwa zagayen karshe a gasar Zakarun Turai REUTERS
Talla

Wannan dai ya ba Barcelona nasarar tsallakewa zuwa zagayen karshe karo na 8 a gasar Turai.

Neymar ne ya jefa wa Barcelona dukkanin kwallayenta a raga gidan Bayern.

Yanzu kuma Barcelona na harin lashe kofuna uku ne a bana, a yayin da ta ke dab da lashe kofin La liga, sannan zata buga wasan karshe da Athletic Bilbao a gasar Copa del Ray a ranar 30 ga wannan watan na Mayu, kafin ta hadu da Juventus ko Real Madrd a wasan karshe a gasar zakarun Turai a ranar 6 ga watan Juni.

Tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola wanda ya kashi a hannun tsoffin ‘yan wasansa ya ce tun da an yi waje da Bayern Munich yana son Barcelona ta lashe kofin gasar a bana.

Guardiola ya taya ‘ya wasan shi na Barcelona murna, tare da yabawa ‘Yan wasan Bayern Munich da suka yi kokarin doke Barcelona a Munich.

Karo na biyar ke nan Bayern na ba Barcelona kashi a Allianz Arena.

A yau Laraba kuma akwai gumurzu tsakanin Real Madrid da Juventus.

Juventus ce ke kan gaba da kwallaye biyu a ragar Real Madrid bayan sun tashi 2 da 1 a karawa ta farko da suka fafata a gidan Juventus.

Wannan ne karo na farko da Juventus ta kai zagayen kusa da karshe a tsawon shekaru 12, lokacin da ta doke Real Madrid, sannan ta sha kashi a hannun AC Milan a wasan karshe da suka fafata a Manchester.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.