Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Barcelona ta lallasa Bayern Munich

Barcelona ta ba Bayern Munich kashi 3 da 0 a wasan farko da suka fafata a zagayen dab da na karshe a gasar zakarun Turai. Messi ya fara bude ragar Bayern Munich da kwallaye biyu tare da mika wa Neymar ya jefa kwallo ta uku bayan an dawo hutun rabin lokaci.

FC Barcelona v Bayern Munich
FC Barcelona v Bayern Munich REUTERS
Talla

Wannan ne kuma karo na 100 da Messi ke haskawa a gasar zakarun Turai, kuma kwallayen da ya jefa a ragar Bayern sun sa ya sha gaban Cristiano Ronaldo da yawan kwallaye 77 a gasar.

‘yan wasan Barcelona dai sun fafata ne da tsohon kocinsu Guardiola wanda ya lashe wa kungiyar kofuna 14 a shekaru 4, kuma wannan ne karon farko da ya kawo ziyara gidan Barcelona bayan ya raba gari da kungiyar.

Guardiola yace zasu yi kokarin mayar da martani da haduwa ta biyu da za su fafatawa a Munich.

Barcelona dai ta rama kashin da ta sha a hannun Bayern Munich ci 7 da 1 gida da waje a 2013.

A ranar Talata Juventus ta doke Real Madrid ne ci 2 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.