Fitattun ‘yan wasar kasar Faransa sun mutu a hatsarin jirgi
Wasu fitattun ‘yan wasan kasar Faransa sun mutu a hatsarin Jirgin sama mai saukar Ungulu a kasar Argentina, lokacin da Jiragen da suke ciki suka yi karo da juna
Wallafawa ranar:
‘Yan wasar da suka hada da Florence Arthaud mai tuka JIrgin kwale-kwale, da Camille Muffat ‘yar wasar ninkaya da ta lashe gasar Olympic dad an damben zamani Alexis Vastine, na daga cikin mutane 10 da suka mutu a hatsarin Jirgin.
Hatsarin kuma ya auku ne a yayin da ‘yan wasar ke daukar Hoton Bidiyo na wani Film da ake shiryawa na Reality TV.
Wannan mutuwar dai ta zama babban abu a kasar Faransa, lura da yadda mamatan suka yi suna a harkokin wasanni a kasar ta Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu