Isa ga babban shafi
Wasanni

Cote D'Ivoire ta yi nasarar zuwa matakin karshe na gasar Afirka

A ci gaba da gasar neman kofin Afirka na kwallon kafa karo na 30 a kasar Equatorial Guinee, a cikin daren jiya kasar Cote d’Ivoire ta yi nasarar zuwa matakin karshe na gasar bayan da ta doke Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ci 3-1. 

'Yan wasan Ivory Coast na murnar samun galaba
'Yan wasan Ivory Coast na murnar samun galaba REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Yaya Toure ne ya soma zura kwallo ta farko a ragar kasar Congo lokacin da aka shiga minti na 20 da soma karawar, to sai dai dan wasan kasar Congo Mbokani Bezua ya rama wannan ci ana minti na 24 da fara fafatawar.

Kafin a je hutu rabin lokaci dan wasan kasar Ivory Coast Gervinho ya sake zura wata kwallon a ragar Congo ana minti na 41 da fara wasan.

Daga bisani dai ‘yan kasar ta Congo sun yi iya kokarinsu domin daukar fansa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci amma hakan ya gagara, domin kuwa dan wasan Ivory Coast mai suna Kanon ya kara jefa wata kwallon ana minti na 68, kuma haka aka ci gaba da wasan har zuwa karshen lokaci Ivory Coast na da ci 3 Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo na da 1.

A yau alhamis kuwa Ghana da kuma Equatorial Guinee ne za su kara da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi domin samun nasarar zuwa matakin karshe na gasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.