Isa ga babban shafi
Champions League

Arsenal ta shiga gasar Zakarun Turai

Alexis Sanchez ya taimakawa kungiyar Arsenal shiga gasar zakarun Turai wanda shi ne ya jefa kwallo a ragar Besiktas ta Turkiya da aka tashi ci 1-0 a filin wasa na Emirate a Ingila. A fafatawar kuma an sake ba Dan wasan Arsenal jan kati Mathieu kamar yadda alkalin wasa ya kori Aaron Ramsey a karawa ta farko.

Dan wasan Arsenal, Olivier Giroud a fafatawarsu da  Besiktas a Istanbul
Dan wasan Arsenal, Olivier Giroud a fafatawarsu da Besiktas a Istanbul REUTERS/Murad Sezer
Talla

Yanzu Besiktas zata tsallaka ne gasar Europa League domin samun hurumi a gasar.
A karon farko kuma tsawon shekaru 16 Athletic Bilbao ta tsallaka gasar tsakarun Turai bayan ta samu sa’ar Napoli ci 3-1 a daren jiya kuma ta tsallake ne da jimillar kwallaye ci 4-2.

Sauran kungiyoyin da suka tsallake sun hada da Kungiyar Malmo ta Sweden da Bayer Leverkusen da kuma Ludogorets da ta yi waje Steaua Bucharest a bugun fanalti.
A yau ne dai a birnin Monaco za’a hada kungiyoyin da zasu kara da juna a zagayen farko a gasar zakarun Turai.

Haka kuma a yau hukumar kwallon Turai zata zabi gwarzon dan wasan Turai tsakanin Cristiano Ronaldo da Arjen Robben da Manuel Neuer a birnin Monaco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.