Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta dauki kofin Community Shield

A ranar lahadin da ta gabata Arsenal da ke rike da kofin kalubale na kasar Ingila, ta doke Man City wadda ke rike da kofin Premier a karawar da suka yi domin daukar kofin Community Shield.

'Yan wasan Arsenal suna murnan lashe kofin FA a Ingila
'Yan wasan Arsenal suna murnan lashe kofin FA a Ingila Reuters
Talla

An dai tashi wasan ci Arsenal na da ci 3 yayin da Man City ke nema, kuma dan wasan Arsenal mai suna Cazorla ne ya zura kwallo ta farko ana minti na 21 da soma fafatawar, yayin da Ramsey ya zura ta biyu a daidai minti na 41, sannan a can minti na 61 Giroud ya kara jefa wata kwallon a ragar Man city, haka dai aka tashi wasan ci 3-0.

Wasannin Sada Zumunci

A wasannin sada zumunci kuwa, a jiya lahadi Liverpoopl ta kasar Ingila ta doke Burussia Dortmund ta kasar Jamus ci 4-0.

Sabon dan wasan da Liverpool ta sayo daga Southampton a kan kudin Fan milyan 20 wato Dejan Lovren na daya daga cikin wadanda suka samu nasarar zura kwallaye a karawar ta jiya.

Chelsea ta yi nasara a wasan sada zumunci da ta buga da Ferencvaros ci 2-1, to sai dai daya daga cikin zaratan ‘yan wasan na Chelsea da bai jima da dawowa a wannan kulob ba wato Didier Drogba, ya samu rauni tun kafin a je hutun rabin lokaci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.