Isa ga babban shafi
Wasanni

An nada Herve Renard a matsayin mai horas da 'yan wasan Cote D'Ivoire

A wannan alhamis hukumomi a kasar Cote D’Ivoire sun bayyana Herve Renard tsohon mai horas da ‘yan wasan kasar Zambia a matsayin wanda zai horas da kungiyar Elephant ta kasar, bayan da Sabri Lamouchi wanda ya jagoranci ‘yan wasan kasar zuwa Brazil ya yi sauka daga kan mukaminsa a cikin wannan wata.

sabon kociyan Ivory Coast, Herve Renard
sabon kociyan Ivory Coast, Herve Renard AFP PHOTO/ KHALED DESOUKI
Talla

Herve Renard dan kimanin shekaru 45 a duniya, za a gabatar da shi a ranar litinin mai zuwa a gaban menama labarai, domin bayyana wa duniya yadda zai farfado da wannan kulob da ake kallo a matsayin zarata a nahiyar Afirka.
Shi dai Herve, ya taba horas dan ‘yan wasan kulob din Sochaux da ke bugawa a rukuni na daya a Faransa, sannan mataimakin mai horas dan ‘yan wasan Black Stars na Ghana, ya kuma zauna a Angola na gajeren lokaci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.