Isa ga babban shafi
Brazil 2014

Brazil da Jamus sun kori Colombia da Faransa

Brazil ta doke Colombia ci 2 da 1 yayin da Jamus ta samu sa’ar Faransa ci 1 da 0 a zagayen kwata Fainal da kasashen suka fafata da gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a kasar Brazil.

Thiago Silva da David Luiz 'Yan wasan Brazil da suke zirara kwallaye biyu a ragar  Colômbia
Thiago Silva da David Luiz 'Yan wasan Brazil da suke zirara kwallaye biyu a ragar Colômbia REUTERS/Jorge Silva
Talla

Thiago Silva da David Luiz ne suka jefa wa Brazil kwallayenta a ragar Colombia wanda ya ba kasar nasarar tsallakewa zuwa zagayen dab da na karshe.

Ana saura minti 10 a kammala wasa James Rodriguez ya rama wa Colombia kwallo guda a bugun daka kai sai mai tsaron gida.

Amma Brazil ba ta ci ribar wasan ba domin an kwashi babban dan wasan kasar Neymar a cikin Makara saboda raunin da ya samu a wasan. Haka kuma Jagoran ‘Yan wasan Brazil Thaigo Silva ya karbi katin gargadi guda biyu matakin da zai haramta ma sa buga wasa da Jamus da ta doke Faransa.

Brazil da Jamus za su maimata tarihi ne inda Brazil ta doke Jamus ci 2 da 0 a karawar karshe a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a shekarar 2002.

Wannan kuma zai kasance karo na biyu da Brazil ke haduwa da Jamus a tarihin gasar cin kofin Duniya.

Daruruwan magoya bayan Jamus suna murnar doke Faransa a gasar cin kofin duniya a Brazil
Daruruwan magoya bayan Jamus suna murnar doke Faransa a gasar cin kofin duniya a Brazil REUTERS/Steffi Loos

Jamus ta samu nasarar tsallakewa ne zuwa zagayen dab da na karshe a bana bayan ta doke Faransa ci 1 da 0 a filin wasa na Maracana a birnin Rio de Janeiro.

Dan wasan Borussia Dortmund Hummels shi ne ya jefa wa Jamus kwallonta a ragar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.