Isa ga babban shafi
Brazil 2014

‘Yan wasan Jamus suna fama da mura

Mai horar da ‘Yan wasan Jamus Joachim Loew yace kusan ‘Yan wasan shi guda bakwai ke fama da mura kafin su fafata da Faransa a zagayen kwata fainal a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a kasar Brazil. Sai dai Kocin bai bayyana sunayen ‘Yan asan ba da suke fama da mura.

Dan wasan Jamus Mesut Ozil na Arsenal
Dan wasan Jamus Mesut Ozil na Arsenal Reuters
Talla

Wannan dai matsala ce ga Jamus idan idan ‘Yan wasan kasar bas u cikin koshin lafiya domin samun jin dadin kece raini da Faransa.

Kocin yace ‘Yan wasan sun kamu da mura ne saboda sauyin yanayi da sanyin AC da suka samu kansu a Brazil.

A yau Juma’a ne Faransa da Jamus zasu fara kece raini a filin wasa na Maracana, daga bisani ne kuma Brazil mai karbar bakuncin gasar ta fafata da Colombia a Forteleza.

Akwai shugaban Kwallon Jamus da ya shammaci Michel Platini shugaban hukumar kwallon Turai inda ya aika masa da sako yana tambayar Platini akan sirrin yadda Jamus za ta doke Faransa.

Nan take ne kuma Platini ya mayar masa da amsa akan, sai idan Jamus ta rama kwallayen da Faransa zata zirara a raga.

Platini tsohon dan wasan Faransa ne wanda sau uku a jere da jere yana lashe kyautar gwarzon Turai.

Amma a zamanin shi sau biyu Jamus ke doke Faransa a gasar cin kofin duniya a zagayen dab da na karshe da aka gudanar a 1982 da 1986.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.