Isa ga babban shafi
Europa League

Benfica da Sevilla sun doke Juventus da Valencia

Benfica da Sevilla sun tsallake zuwa buga wasan karshe a gasar Europa League bayan Benfica ta yi waje da Juventus, Sevilla kuma ta sha da kyar a hannun Velencia.

Ezequiel Garay na Benfica a karawarsu da Juventus
Ezequiel Garay na Benfica a karawarsu da Juventus REUTERS/Hugo Correia
Talla

A karawar da aka yi a jiya Alhamis, Benfica da Juventus sun tashi ne babu ci amma tun a karawa ta farko ne Benfica ta doke Juventus ci 2-1.

Wannan kuma shi ne ya haramtawa Juventus buga wasan karshe da za’a gudanar a filinta a Italiya a ranar 14 ga watan Mayu.

Sevilla ta sha da kyar ne a hannun Valencia domin ana dab da kammala wasa ne dan kasar Kamaru Stephane Mbia ya jefa kwallo a ragar Valencia bayan Valencia ta zirara kwallaye 3 a gidanta.

An kammala fafatawan ne da jimillar kwallaye ci 3-3, kuma Sevilla ta tsallake zuwa buga wasan karshe ne saboda kwallaye biyu da ta fara zirawa a ragar Velencia a karawa ta farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.