Isa ga babban shafi
Tennis

Djokovic ya lashe kofin Miami Masters

Novak Djokovic ya lashe kofin Miami Masters bayan ya doke Rafael Nadal a karawar karshe ci 6-3 6-3. Wannan ne karo na hudu da Djokovic ke lashe kofin gasar da ake kira Sony Open. Kuma duka duka mako biyu ke nan da dan wasan na Serbia ya lashe kofin Indian Wells bayan ya doke Roger Federer a wasan karshe.

Novak Djokovic na Serbia rike da kofin Sony Open da ya lashe a Miami bayan ya doke Rafael Nadal
Novak Djokovic na Serbia rike da kofin Sony Open da ya lashe a Miami bayan ya doke Rafael Nadal Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.