Isa ga babban shafi
Tennis

Serena ta doke Sharapova a Miami

Serena William ta tsallake zuwa buga wasan karshe a gasar Miami Masters bayan ta lallasa Maria Sharapova ta Rasha ci 6-4 ci 6-3 a wasan dab da na karshe. Serena zata fafata ne da Li Na ta China a wasan karshe a karawar Jaruman tennis na duniya.

Serena Williams Yar wasan Tennis ta Amurka
Serena Williams Yar wasan Tennis ta Amurka Reuters
Talla

A bangaren maza kuma Rafael Nadal ya tsallake ne zuwa zagayen dab da na karshe a Miami bayan ya doke dan kasar Canada Milos Raonic, Nadal zai hadu yanzu da Tomas Berdych a zagaye na gaba.
.
Idan an jima ne kuma za’a yi fafatawa tsakanin Kei Nishikori na Japan Dan kasar Serbia Novak Djokovic.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.