Isa ga babban shafi
Tennis

Sony Open: Nadal ya tsallake zuwa Kwata Fainal

Rafeal Nadal ya bi sahun Novak Djokovic da Andy Murray da Roger Federer zuwa zagayen kwata Fainal a gasar Sony Open da ake gudanarwa a Maimi bayan ya doke Fabio Fognini na Italia. A zagaye na gaba Nadal zai hadu ne da Milos Raonic na Canada wanda ya doke Benjamin Becker ci 6-3 da 6.4.

Dan wasan Tennis Rafael Nadal
Dan wasan Tennis Rafael Nadal Geoff Burke-USA TODAY Sports
Talla

Roger Federer ya tsallake ne bayan ya doke Richard Gasquet na Faransa, yayin da Andy Murray mai rike da kofin gasar ya yi waje da Jo-Wilfried Tsonga na Faransa. Djokovi kuma ya doke Tommy Robredo ne na Spaniya ci 6-3 da ci 7-5.

A bangaren mata Serena Williams ta tsallake zuwa zagayen dab da na karshe a gasar Sony Open bayan ta doke Angelique Kerber ta Jamus ci 6-2 6-2 a kwata Fainal.

Yanzu kuma Serena Williams Jarumar Tennis din ta duniya zata hadu ne da abokiyar hammayrta Maria Sharapova, ta Rasha a zagayen dab da na karshe bayan Sharapova ta doke Petra Kvitova ta Jamhuriyyar Czech.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.