Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Mun riga mun tsallake-Ronaldo

Cristiano Ronaldo na Real Madrid yace nasarar da suka samu akan Schalke 04 ta Jamus ci 6-1, babu shakku sun tsallake zuwa zagayen kwata Fainal, yana mai cewa wannan aiki ne na hadin kan dukkanin ‘Yan wasan Real Madrid da ke cikin filin wasa.

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo
Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo REUTERS/Ina Fassbender
Talla

Bayan karawa tsakanin Real Madrid da Schalke 04 akwai likita da ke kula da lafiyar ‘yan wasan kwallon kafa da ya yi murabus daga aikinsa a hukumar kungiyar kwallon kafa a kasar Jamus saboda wani hoton Dan kasar Ghana Kevin-Prince Boateng da aka wallafa a Jarida yana shan barasa kuma rike da Karen Sigari.

Boateng yana cikin tawagarar kungiyar Schalke da suka sha kashi a hannun Real Madrid ci 6-1, wasa mafi muni a tarihi da wata kungiyar Jamus ta sha kashi a gasar zakarun Turai.

Jaridar Daily Bild ce ta buga labarin, kuma an dauki hoton Boateng ne a lokacin da ake diba lafiyar shi. Kungiyar Schalke tace zata dauki mataki na Shari’a domin an dauki hoton rayuwar dan wasan ne ba tare da sanin shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.