Isa ga babban shafi
Tennis

Li Na da Wawrinka suka lashe Australian Open

A bana sabbin hannu ne aka samu da suka lashe gasar Australian Open a bangaren maza da mata da ake gudanarwa a Melbourne. Li Na ta China ita ce ta lashe kofin Mata bayan ta lallasa Dominika Cibulkova ta Slovakia ci 7-6 (7/3), 6-0.

Stanislas Wawrinka dauke da kofinsa na Australian Open
Stanislas Wawrinka dauke da kofinsa na Australian Open REUTERS/David Gray
Talla

A bangaren maza kuma Wawrinka ne ya lashe kofin gasar Australian Open karo na farko wanda ya samu sa’ar zakaran Tennis na duniya Rafael Nadal a fafatawar karshe.
A jawabinta bayan samun nasara Li na ta china cikin raha ta godewa mai horar da ita da mijinta tare da mika godiya ga abokiyar karawatara.

“Ina taya Dominic murna domin ta nuna bajinta, ina mata fatan alheri anan gaba” inji Li Na.

Wannan nasarar da Li Na ta samu yanzu ta hauro zuwa matsayi na uku a jerin jaruman tennis na duniya bayan Victoria Azarenka ta biyu da Serena Williams jarumar Tennis ta duniya.

A shekarar 2011 dai Li Na ita ce ta farko daga yankin Asiya da ta taba lashe kofin manyan gasannin Tennis na duniya inda ta lashe French Open da ake kira Rolland Garros a Faransa.

Cibulkova wacce ta sha kashi a hannu Li Na ita ce ta lallasa Maria Sharapova da Radwanska, kuma wannan ne karo na farko da aka samu wata daga kasar Slovakia da ta kai zagayen karshe a manyan gasannin Tennis na Grand Slam.

A bangaren maza Stanislas Wawrinka ne ya lashe kofin gasar a karon Farko wanda ya samu sa’ar Rafael Nadal a fafatawar karshe.

A wasan dai Nadal ya yi fama da rauni ne a kashin bayansa inda tun a tashin farko zagaye na daya da na biyu Wawrinka ya doke shi 6-3, 6-2, amma a zagaye na uku Nadal ne ya samu nasara ci 3-6, a zagayen karshe kuma Wawrinka ya doke Nadal ne ci 6-3 a fafatwar da suka kwashe tsawon sa’o’I 2 da minti 21.

Nadal dai ya nemi ya lashe manyan gannin Tennis na duniya Grand Slams har guda 14. Kuma cikin kofunan duka guda daya kacal ne ya lashe a Australian Open amma shi ne ya lashe kofuna 7 a Rolland Garros da ake gudanarwa cikin turda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.