Isa ga babban shafi
Tennis

Cibulkova ta lallasa Radwanska a Australian Open

‘Yar wasan Slovakia Dominika Cibulkova ta lallasa Radwanska, ci 6-1, 6-2 a gasar Kwallon Tennis ta Australian Open da ake gudanarwa a Melbourne. Yanzu dai Cibulkova ta tsallakewa ne zuwa zagayen karshe inda zata hadu da Li Na ta China.

Agnieszka Radwanska a lokacin da ta doke  Victoria Azarenka
Agnieszka Radwanska a lokacin da ta doke Victoria Azarenka Reuters
Talla

Radwanska, ita ce ta yi waje da Azarenka jarmumar Tennis ta duniya amma a yau ita ma ba ta sha da dadi ba.

Idan an jima kuma akwai karawa tsakanin Tomas Berdych da Stanislas Wawrinka a bangaren maza zagayen dab da na karshe.

A gobe Juma’a ne kuma za’a kece raini tsakanin Roger Federer da Rafael Nadal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.