Isa ga babban shafi
Tennis

Sharapova ta fice Australian Open

Bayan ficewar Serena Williams a wasannin gasar Australian Open da ake gudanarwa, sauran manyan jaruman Tennis din na duniya a bangaren Mata da suka rage sun fara shan kashi, inda a yau Litinin Maria Sharapova ta Rasha ta fice gasar bayan ta sha kashi a karawarta da Dominika Cibulkova ta Slovakia a zagaye na hudu.

Maria Sharapova a fafatawarta da Dominika Cibulkova a Australian Open
Maria Sharapova a fafatawarta da Dominika Cibulkova a Australian Open REUTERS/Petar Kujundzic
Talla

Amma Victoria Azarenka ta samu nasarar tsallakewa zuwa zagayen kwata Fainal bayan ta doke Sloane Stephens ta Amurka.

Serena tace rauni ya sa aka doke ta, haka ma Sharapova tace akwai raunin da ta samu a kugunta, kodayake ‘Yar wasan ta Rasha ba tace shi ne dalilin da ya sa aka samu gabalabarta ba.

Yanzu Serena da Sharapova sun bude wa Azarenka kofar lashe kofin gasar, domin ana ganin dama sune za su iya taka wa Azerenka burki.

A karawar kwata Fainal Azarenka ta Belarus za ta fafata ne da Radwanska, waccce ta lallasa Muguruza ta Spain.

A bangaren maza a zagayen Kwata Fanial Roger Federer zai hadu da andy Murray wadanda dukkaninsu zarata ne a fagen kwallon Tennis.

A yau Litnin ne Federer ya yi waje da dan wasan Faransa Jo-Wilfried Tsonga a yayin da Rafael Nadal ya tsallake zuwa zagayen Kwata Fainal inda zai hadu da Grigor Dimitrov na Bulgeria bayan Nadal ya sha da kyar a fafatawar shi da Nishikori na Japan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.