Isa ga babban shafi
Tennis

Nadal da Federer da Murray sun tsallaka zagaye na hudu a Australian Open

Zakaran Tennis na duniya Rafael Nadal ya bi sahun Andy Murray da Roger Federer zuwa zagaye na hudu bayan samun nasara a wasan da ya lallasa Dan wasan Faransa Gael Monfils ci 6 da 1, 6 da 2, 6 da 3 a gasar Australian Open a ranar Assabar.

Zakaran Tennis na duniya Rafael Nadal
Zakaran Tennis na duniya Rafael Nadal REUTERS/Jason Reed
Talla

A zagaye na hudu Nadal zai fafata ne tsakanin shi da Kei Nishikori na Japan wanda ya doke Dan wasan Amurka Donald Young

Murray, wanda sau hudu yana buga wasan karshe a gasar Australian Open ya doke Feliciano Lopez ne na Spain kamar yadda Federer ya lallasa dan wasan rasha Teymuraz Gabashvili.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.