Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Manchester ta lallasa Kitchee FC a Hong Kong

Manchester United ta doke kungiyar Kitchee FC ci 5-2, a Hong Kong wanda kuma wannan ne karo na biyu da David Moyes ke samun nasara a matsayin kocin kungiyar, kafin a fara wasannin Premier.

Sabon kocinManchester United David Moyes
Sabon kocinManchester United David Moyes Reuters/Phil Noble
Talla

Tun kafin tafiya hutun rabin lokacin ne Danny Welbeck da Chris Smalling da Fabio Da Silva da Adnan Januzaj suka jefawa Manchester kwallaye 4 a raga.

Yanzu dai Tawagar Manchester ta kammala ziyara a yankin Asiya da Australia, amma a ziyarar, Manchester ta samu nasara sau biyu da yin kunnen doki biyu tare da shan kashi sau biyu.

Har yanzu dai David Moyes yana ci gaba da farautar dan wasan Barcelona Cesc Fabregas, duk da Barcelona tace dan wasan ba na sayarwa ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.